Posts

Showing posts with the label Kirfi

Ni Na Dora Bala A Gwamna, Kuma Ni Zan Sauke Shi – Tsohon Wazirin Bauchi

Image
  Tubabben Wazirin Bauchi, Muhammadu Bello Kirfi, ya sha alwashin sai ya cire Gwamnan Jihar, Bala Mohammed, daga mukaminsa kamar yadda shi ma ya cire shi daga mukaminsa. Kirfi ya bayyana haka ne sakamakon tube masa rawani da Masarautar Bauchi ta yi masa a matsayin Wazirin Bauchi. Masarautar Bauchi ta tube tsohon Wazirin ne saboda abin da ta kira da rashin biyayya ga Gwamnan Jihar. Da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi, Kirfi ya ce, “Hanyar da na shigar da shi ofis, ta nan zai bi ya fita. “Na dauki abin da ya faru da ni a matsayin karamin al’amari saboda wani abu na damuna a raina. “Ina daya daga cikin wadanda suka tsaya masa ya samu Gwamna, kuma na ji takaicin abin. “Wannan shi ne iya abin da zai iya yi, ba komai ba ne wannan saboda babu wata riba da nake samu (a matsayin Waziri) a Fadar Sarki.” Ya ce ya tka muhimmiyar rawa a zama gwamnan da Bala ya yi a 2019, saboda a lokacin yana matukar neman goyon baya don cika burinsa na siyasa. “Na yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar...