Posts

Showing posts with the label El-Rufa'i

Babu Wanda Nake Tsoro —El-Rufai Ga ‘’Yan Fadar Buhari’

Image
  Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kalubalancin ’yan fadar shugaban kasa da yake zargi da zagon kasa ga takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da ke tafe.  Tun a ranar Laraba El-Rufai ya fara tayar da kura da zargin cewa akwai jami’an Fadar Shugaban Kasa da ke neman yi wa takarar Tinubu kafar ungulu. A wata hirarsa da Sashen BBC na Hausa, an ji shi yana cewa, “Na rantse babu mahalukin da nake tsoro a duk fadin kasar nan. “Don ana ganin girmn mutum ba soronsa ake ji ba; Amma idan muna girmama mutum, amma yana nuna shi ba babba ba ne, to wallahi za mu ake shi.” Ana ganin kalaman nasa kari ne a kan zargin wadanda yake zargi a fadar shugaban kasa, da ya cesuna neman tadiye inubu. BBC sun fitar da somin-tabin hirar ce kafin a fitar da shi gaba dayansa. A ranar Laraba, a waya hira da shirin Sunrise Daily na gidan alabijin na Channels ne El-Rufai ya yi zargin akwai magoya baan wadanda suka nemi takarar shugaban kasa a APC wanda Tibubu a lashe da ke fakewa da Shugaba Buhari domin ...

Akwai Makiyan Tinubu A Fadar Shugaban Kasa – El-Rufa’i

Image
  Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai makiyan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Shugaban da suke kokarin ganin sun kai shi kasa. Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na  Sunrise Daily  da safiyar Laraba. El-Rufa’i ya ce mutanen, wadanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani na APC. Ya kuma ce mutanen na fakewa da bukatar ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace. Ya ce, “Na tabbatar a cikin Fadar Shugaban Kasa akwai masu son mu fadi zaben nan, saboda bukatarsu ba ta biya ba, an kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani. “Wadannan mutanen na kokarin fakewa da bukatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu; wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Najeriya ta kashe makudan kudade abu ne da dukkanmu mun dade da amincewa a cire shi. “Sai da ma na tattauna da Shuga...

El-Rufai ya yi wa fursunoni 11 afuwa a Kaduna

Image
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yin afuwa ga fursunoni 11 daga gidajen yarin jihar domin murnar sabuwar shekarar 2023. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwaman kan kafofin yaɗa labarai na gwamnan jihar Mista Muyiwa Adekeye ya fitar. Afuwar ta shafi fursunonin da suka nuna kyakkyawan hali da waɗanda suke fama da rashin lafiya kamar yadda sanarawar ta bayyana. Haka kuma gwamnan ya nemi al'ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya, tare da fatan cewa aikin da ya faro tun a shekarar 2015 domin inganta rayukan al'umma jihar za su ci gaba a gwamnati mai zuwa. (BBC HAUSA)