Posts

Showing posts with the label Diezani

Birtaniya Ta Gurfanar Da Diezani A Gaban Kotu Kan Zargin Almundahana

Image
Kasar Birtaniya ta gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin rashawa lokacin da take Minista. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ’yan sandar kasar sun ce sun maka ta a kotun ne saboda suna zargin ta karbi cin hanci a wasu kwangilolin man fetur da iskar gas. Diezani, mai shekara 63 a duniya, na daya daga cikin kusoshi a gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan. A zamanin mulkin tsohon Shugaban, Diezani ta rike mukamin Ministar Mai ta Najeriya daga 2010 zuwa 2015, sannan ta rike matsayin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC). A cewar Shugaban Hukumar Yaki da Laifuffuka ta Birtaniya (NCA), Andy Kelly, “gurfanarwar da aka yi wa Diezani wata somin-tabi ce na wani zuzzurfan bincike na kasa da kasa da aka dade ana yi.” Hukumar dai ta ce ana zargin Diezani da karbar akalla tsabar kudi har Fam din Ingila 100,000 da wasu motoci da hawa jirgin da ba na ’yan kasuwa ba,

Mutum 26 Sun Saye Kadarorin Diezani Da Aka Yi Gwanjonsu

Image
Akalla mutum 26 ne suka saye kadarorin da gwamnati ta yi gwanjonsu bayan kwato su daga hannun barayin gwamnati. Kadarorin sun hada da gidaje da filaye da aka kwato daga tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Allison-Madueke, a Abuja da sauran wurare. A shekarar da ta gabata Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta yi gwanjon kadarorin ga masu son sayen su. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, a ranar Litinin hukumar ta fara mika kadarorin da aka saye na Legas da Abuja da Fatakwal da Kano da sauran wurare. Sai dai kadarorin sun yi kwantai a ranar Liinin da aka yi gwanjon su, ko mutum guda ba a samu da ya sayi ko da daya daga cikinsu ba. Amma mutum shida daga cikin 90 da suka nema suka yi nasara a rukuni na hudu a ranar Talata. Da yake sanar da wadanda suka yi nasara a ranar Alhamis, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce kadarori 26 sun samu shiga, 13 kuma sun gaza, saboda rashin cika ka’ida da sauransu. A cewar Uwujaren, “Kadarori 39 ne a rukuni na biyar wadanda ke a wurare da

EFCC Ta Yi Gwanjon Kadarorin Su Diezani A Kasuwa

Image
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da yin gwanjon wasu kadarorin da ta kwace daga hannun ’yan siyasa da ’yan kasuwa ga ’yan Najeriya masu bukatar saya. Hukumar ta ce kadarorin dai na jibge ne a Jihohin Legas da Ribas da Abuja da Anambra da Gombe da Ebonyi da Kaduna da Delta da Edo daKwara da Kuros Riba da Osun da kuma Oyo. Aminiya ta gano cewa daga cikin kadarorin har da na tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Allison-Madueke, wadanda hukumar ta ce an mallake su ta haramtacciyar hanya. A wata sanarwar da hukumar ta wallafa ranar Asabar, EFCC ta ce daidaikun mutane da kuma kamfanoni da kungiyoyin da ke son sayen kayan da aka yi gwanjon dole ne su kasance ba a taba daure su ba a baya. A cewar sanarwar, ga masu bukatar sayen kadarorin, za su iya cike fom din neman saye da za a iya samu a shafin hukumar na www.efcc.gov.ng, kafin daga bisani a gayyace su don ganin kadarorin da ido. Kadarorin da aka yi gwanjon nasu sun hada da wani gida a rukunin gidaje na Herit