Posts

Showing posts with the label ANCOPPS

An Rantsar Da Shugabannin Riko Na Kungiyar Shugabannin Makarantun Sakandire Ta Kasa Reshen Kano

Image
An rantsar da sabbin shugabannin kungiyar Malaman Makarantun Sakandire  (ANCOPSS) reshen Kano a matsayin masu rikon kwarya domin tafiyar da harkokin kungiyar na tsawon watanni uku kafin babban zabe. A sanarwar da daraktan wayar da kawunan al'uma na ma'aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanyawa hannu, yace alIdan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne ma’aikatar ilimi ta jihar ta sanar da rusa Shugabancin kungiyar  da ya gabata tare da kafa sabbin riko da za su yi aiki na tsawon watanni 3 a shirye-shiryen zaben shugabannin zartarwa. Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da sabbin mambobin zartaswar, kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya ci gaba da cewa nadin sabbin mambobin ya kasance bisa cancanta da kuma wani bangare na kokarin tsaftace tsarin zabe na daukacin jami’an da ke karkashin ma’aikatar. Don haka Umar Doguwa ya bayyana cewa sabbin masu rike da mukaman ANCOPSS sun kasance shirye-shiryen tunkarar zaben, inda suka rage a matsayinsu na hada ka