Abdulmumin Kofa ya Gabatar da kudirin kafa Jami'a a Kofa da Karin wasu Kudurorin 14
Abdulmumin Jibrin Kofa PhD, ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓar Kiru/Bebeji, Kano, ya kafa tarihin gabatar da kudurori har guda 15 a zauren majalisar, kuma tuni dukkansu suka tsallake matakin karatu na farko a cikin mako ɗaya. Daga cikin ƙudurorin har da na kafa Jami’ar Kasuwanci ta Kofa, Bebeji, Kano, wanda shi tuni ya tsallake matakin karatu na biyu, Sannan akwai wasu ƙudurorin da suka shafi yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, bunƙasa harkokin zuba jari da kasuwanci, bayar da ilimin kyauta da kuma ilimin gaba da sakandare da dai sauransu. Ɗan Majalisar dai ya ɗauki lokaci sosai wajen yin nazari mai zurfi kan buƙatun mutanen mazaɓarsa, kafin ya gabatar da ƙudurorin a majalisa. Jami’ar Kasuwancin za ta kasance irinta ta farko wajen horar da jajirtattun matasanmu su kasance maso dogaro da kai a harkar kasuwanci, ta yadda za su yi shi bisa ilimi sannan su yi gogayya da takwarorinsu a kasuwannin ciki da wajen Najeriya. Kano dai ita ce ba...