Posts

Showing posts with the label 'Yan sanda

'Yan sandan Najeriya sun ceto mutane 58 daga hannun 'yan bindiga

Image
  ‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun ceto mutane 58 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Kogi, yayin da daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da sun ya rasa ransa yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’addan A cikin wata sanarwa da kakakin rundinar ‘yan sandan jihar Josephine Adeh ta fitar a wannan Lahadin, ta ce wannan nasara da suka samu wani bangare ne na aikin hadin gwiwa tsakanin rundunar da sauran jami’an tsaro, tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarautan jihar.  Adeh ta ce lamarin ya faru ne a dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu mai nisan kilomita 145 daga bababban birnin tarayya kasar.  A cewarta, an yi musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da kuma jami’an tsaro kuma daga bisani suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.   Sai dai bata bayyana inda aka sace mutanen ba da kuma tsawon lokacin da suka dauka a hannun ‘yan ta’addan.   RFI

Zaben Adamawa: An Ba Da Belin Kwamishina Hudu

Image
  ’Yan sanda sun bayar da belin Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, bayan da ya yi kwana uku a tsare a hannunsu. ’Yan sanda sun cafke shi ne kan wata sanarwa mai cike da rudani da ya yi  cewa Sanata Aisha Dahiru Binani ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, alhali ba a kammala karbar sakamakon karashen zaben ba. Tun a lokacin INEC ta soke sanarwar, sannan ta bukaci ya gabatar da kansa a hedikwatarta da ke Abuja, amma maimakon ya je, sai ya yi layar zana. Daga bisani hukumar ta rubuta Shugaban ’Yan Sandan Najeriya wasikar neman ya binciki kwamishinan zaben, kan yamutsa hazon da ya yi. Amma wata wasika da ya aike wa shugaban ’yan sanda, Hudu ya ce ya yi sanarwar ne a bisa doka, saboda dalilan tsaro. A ranar Talala ’yan sanda suka sanar cewa sun kama Hudu, wanda ya ce ba ya nadamar sanarwar da ya ya yi cewa Binani ta ci zabe. Amma kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Juma’a cewa rundunar ta bayar da belin kwamishinan zaben.

Za Mu Kama Duk Wanda Ya Dauki Makami Ranar Zabe A Kano —’Yan Sanda

Image
  Mataimakin babban sufeto-Janar na ’yan sanda DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaben shekarar 2023 a yankin jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu, da su kauce wa yin wani abu da zai tada hankulan masu zabe.  DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa shugaban ’yan sanda Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargadi ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su ja wa magoya bayansu kunne gabanin zaben da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023. Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu. Ya kara da cewa fatansu, shi ne a yi zabe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba. “Duk wani dan siyasa in dai yana son ci gaban Kano, to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya. “Kuma na zo da jawabi, in gargade su, Wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina, “Saboda haka ina tabbata