Mun Kama Bako Da Kullin Hodar Iblis 105 Daga Brazil —NDLEA
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama kullin hodar iblis 105 a cikin kayan wani wanda ya dawo daga kasar Brazil a Babban Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya sanar ranar Lahadi a Abuja cewa sun kama wanda ake zargin ne ranar Kirsimeti. Ya ce wanda ake zargin na daga cikin fasinjojin da suka dawo daga birnin Sao Paulo na kasar Brazil. A cewarsa, bayanan sirrin da suka samu sun taimaka wajen kama wanda ake zargin a filin jirgin. Ya ce, saura kiris ya sha sakamakon babu abin da suka gano a binciken farkon da suka yi masa. Da aka tsananta bincike a kansa karo na biyu, sai aka gano hodar iblis din da yake dauke da ita, in ji jami’in. Shugaban NDLEA na Kasa, Birgediya-Janar Buba Marwa (Murabus), ya sha nanata cewa ba za su raga wa masu fataucin miyagun kwayoyi ba ko’ina suke a fadin kasa. (AMINIYA) (NAN)