Kungiyoyi da dama sun so daukata amma na yi wa Al-Nassr alkawari - Ronaldo


Cristiano Ronaldo ya ce kungiyoyin kwallon kafa da dama a sassan duniya sun nuna sha’awar daukar sa amma ya yanke shawarar sanya wa Al-Nassr hannu.

A lokacin da Al-Nassr ta gabatar da shi a matsayin dan wasanta a gaban dubban magoya bayan kungiyar a ranar Talata, Ronaldo ya bayyana cewa kungiyoyi a nahiyar Turai da Brazil Amurka da Australia da Portugal sun nemi su dauke shi amma ya zabi zuwa Saudiyya.

Jaridar Aminiya ta rawaito Ronaldo na cewa “Kamar yadda na fada a baya wannan dama ce a gare ni ba wai a harkar kwallon kafa ba, dama ce da zan sauya tunanin matasa masu tasowa.

“Kungiyoyi da dama daga Nahiyar Turai da Brazil da Amurka da Australia da ma Portugal son so dauka ta amma na yi wannan kungiya alkawari.


“Na san abin da nake so da wanda ba na so, kuma wannan babban kalubale ne a gare ni na zuwa wannan kasa, ba don komai ba sai don na kara samun ilimi.

“Ina son sabon yanayi, kasa don cimma wani buri na daban tare sa Al-Nassr, wannan shi ne dalilin da ya sa na rungumi wannan dama,” in ji Ronaldo.

Ronaldo, dan shekara 37 a duniya, ya rattaba hannun zama a Al-Nassr na tsawon shekara biyu da rabi bayan raba gari da Manchester United a watan Nuwamban 2022.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki