Posts

Showing posts with the label Coronavirus

Fiye da kashi 48 na al'ummar Afrika ba sa samun kulawar lafiya- WHO

Image
  Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ‘yan Afrika miliyan 672 wanda ke wakiltar kashi 48 na al’ummar nahiyar basa samun kulawar lafiyar da ya kamata yayinda suke rayuwa cikin cutuka. WHO ta ce dai dai lokacin da kasashe ke baje hajar gagarumin ci gaban da suka samu a bangaren kiwon lafiya, yayin bikin ranar Lafiya ta Duniya har yanzu Afrika na ganin mummunan koma baya a bangaren. Daraktar hukumar WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta ce bangaren kiwon lafiya na ci gaba da samun koma baya a nahiyar wanda ke da nasaba da rashin kulawar shugabanni don habaka sashen. A sanarwar da ta fitar a ranar lafiya ta Duniya wato World Health Day da ke gudana a kowacce ranar 7 ga watan Aprilu, shugabar ta WHO reshen Afrika, ta ce gazawar bangaren lafiya ya haddasa karuwar cutuka a sassan nahiyar da kuma tsanantar cutuka masu hadari. Dr Matshidiso Moeti ta ce abin takaici yadda hatta kananun cutukan da basu kai su yi kisa ba, su ke iya kashe tarin jama’a a nahiyar ta Afrika saboda gurguncewar b...

Dan Takarar Shugaban Kasa na ADC ya kamu da cutar Corona

Image
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya kamu da Coronavirus bayan sakamakon gwaji ya tabbatar yana dauke da kwayoyin cutar. Mista Kachikwu ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya fitar a ranar Asabar, yana mai gargadin ’yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan don annobar na iya dawowa. Ya bayyana cewa tuni ya killace kansa kuma ya daina halartar tarukan jama’a da duk wasu harkalloli da suka danganci cudanya da al’umma. Dan takarar ya ja hankalin ’yan Najeriya a kan kada su kuskura su yi wa cutar Coronavirus rikon sakainar kashi. Ya ce a halin yanzu alkaluman masu kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa cikin makonnin baya–bayan nan ko’ina a fadin duniya. “Bai kamata ’yan Najeriya su yi kasa a gwiwa ba duk da cewa gwamnati ta sassauta dokokin COVID-19. “Tsare-tsare da kuma tanadin da gwamnati ta yi a fannin kiwon lafiyarmu ba zai haifar da da mai ido ba a yayin da wannan annoba ke neman sake barkewa musamman a daidai lokacin da kwararrun masu kula da hark...