Gwamna Abba Kabir Ya Kaddamar Da Rabawa Daliban Sakandare JAMB 6,500 Kyauta
Ta hanyar samar da karin damammaki na neman ilimin manyan makarantu a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf a yau ya kaddamar da rabon fom din JAMB kyauta ga daliban makarantun sakandire 6,500 a wani taron da ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano. Cikin wata sanarwa da kakakinsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai ya nakalto Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafin yana mai cewa, “Yayin da muke raba fom din JAMB kyauta a yau ga ‘yan jihar Kano 6,500, bari na tabbatar da hakan alama ce ta jajircewar gwamnatinmu alÆ™awarin saka hannun jari a makomar yaranmu “Mun yi imanin cewa ilimi ginshikin ci gaba ne, kuma idan aka ba wa dalibanmu ilimi, yaranmu za su samu ilimi mai inganci, muna aza harsashin samar da ci gaba mai dorewa a jiharmu ta Kano.” Inji Gwamna Abba. Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen yin karin haske kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen bunkasa fannin ilimi a cikin watanni goma da suka hada da; sake...