Gidan Yari Zan Jefa Duk Wanda Ya Karkatar Da Kayan Tallafi —Bago
Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya ce duk wanda ya kuskura ya karkatar da kayan tallafin da gwamantin tarayya ta bayar a jihar, sai an daure shi a gidan yari, komai girman matsayinsa. Gwamna Bago ya bayyana wa ’yan jarida cewa daga jami’an gwamnati zuwa sarakunan gargajiya, duk wanda aka kama ya karkatar da kayan da gwamnatin tarayya ta bayar domin rage wa talakawa halin matsin da suka shiga a sakamakon janye tallafin mai, to babu makawa gidan yari ne makomarsa. Masu makarantun kudi sun koka kan hana su karin kudin makaranta a Kano Ta’addanci: Ba don taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba da mun banu — Tinubu Gwamnan ya sanar da haka ne bayan ya ba da hutun kwana uku domin ma’aikatanta su sami zuwa karbar kayan tallafin da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 3.6. Ya ce hutun na ranar Laraba da Alhamis da Juma’a zai ba wa ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa damar zuwa mazabunsu domin sanya ido da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a wajen rabon kayan. Gwamnan ya bayyana cewa jiha...