Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Bayar Da Umarnin Yin Bincike Kan Yankar Albashin Ma'aikata
… Ya Kaddamar da Kwamitin Bincike da Zai Gabatar da Rahoto Cikin Kwana Bakwai Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana takaicinsa kan rahotannin da suka nuna ana rage albashin wasu ma’aikatan gwamnati ko kuma hana su albashinsu gaba ɗaya, yana mai cewa hakan babban cin zarafi ne ga haƙƙin ma’aikata kuma cin amanar jama’a. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis. Gwamna Yusuf, wanda ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan labarin cewa wasu ma’aikata sun kwashe watanni ba tare da an biya su haƙƙinsu ba, ya yi alkawarin binciko masu hannu a wannan aika-aika tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansu. “Wannan gwamnati ba za ta lamunci zalunci ga ma’aikata ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika, doka za ta yi aiki a kansa ba tare da rangwame ba,” in ji gwamnan. A wani mataki na kawo ƙarshen wannan matsala, gwamnan ya kaddamar da wani kwamitin bincike mai ƙarfi don gano musabbabi...