Mun Kashe $1bn Wajen Kwato Yankunan Da ’Yan Ta’adda Suka Mamaye – Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya ta kashe sama da Dala biliyan daya wajen sayen makaman da ta yi amfani da su wajen yaki da ’yan ta’adda tun 2015. Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata sa’ilin da yake jawabi a wajen Babban Taron Zaman Lafiya na Afirka na 2023, da ya gudana a birnin Nouakchott, Jamhuriyar Musulunci ta Murtaniya. Shugaban wanda aka karrama da lambar yabo ta “Karfafa Zaman Lafiya a Afirka” a Abu Dhabi, ya ce akwai bukatar a rungumi dabi’ar karrama juna da mutuntawa a makarantu, musamman kuma a tsakanin matasa. Haka nan, ya yi kira ga shugabanni da su bai wa rayuwar matasa muhimmanci ta hanyar horar da su sana’o’in hannu domin maganin zaman kashe wando. Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, Buhari ya ce dole a ba da himma wajen hana ta’ammali da kananan bindigogi da sauran makamai a cikin al’umma. Kana ya bukaci yayin taron kasashen Afirka na gaba, a dauki matakin lalubo hanyar magance matsalolin da ke ci gaba ...