Labari da dumiduminsa : Kotu ta bada umarnin mayar da Muhuyi Magaji matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.
Kotun ma'aikata ta kasa da ke zamanta a Kano ta umurci gwamnatin jihar da ta mayar da korarren Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Muhuyi Magaji Rimingado daga kan mukaminsa ba tare da bata lokaci ba. SOLACEBASE ta rawaito cewa kotun a ranar Talata karkashin jagorancin mai shari’a Ebeye David Eseimo ta yanke hukuncin cewa tsige shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Muhuyi Rimingado daga mukaminsa ya sabawa doka, ba komai bane. Idan dai za a iya tunawa Muhuyi Magaji Rimingado ya maka gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar Kano da kuma babban lauyan gwamnatin jihar gaban kotu suna kalubalantar tsige shi daga mukaminsa. Kotun ta karba kuma ta amsa bukatu da mai da’awar ya yi a kan wadanda ake tuhuma. Ta yanke hukuncin cewa wanda ake kara na biyu ba shi da hurumin bayar da shawarar korar wanda ake tuhuma ba tare da fara sauraren karar ba ta hanyar da ya dace ya kare kansa. Akwai cikakken labarin zai zo muku nan ...