DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaÉ“en gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar. Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naÉ—i hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riÆ™a wallafa shi a shafukan sada zumunta. Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar TaÉ“ule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waÉ—anda ta kama. “Cikin waÉ—annan saÆ™onnin masu haÉ—ari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu. “WaÉ—anda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaÉ“en gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar. “Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai ...