Hukumar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ta yi Allah wadai kan sakacin da wani likita ya yi lokacin da yake kula da lafiyar wani jariri
Jaririn wadanda aka haifa makon da ya gabata ya zo da wata matsala wadda ta bukaci yi masa gwaji ta hanyar daukar jininsa a inda likitan ya shiga dimuwa wanda ya haifar da abin da ya faru.
A cikin sanarwar da shugabar sashen hulda da jama’a ta Asibitin Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi ta sanyawa hannu, Hukumar Asibitin ta girgiza da Jin Wannan mugun labari Wanda a shekaru talatin da uku da kafuwar Asibitin Hakan bai tabar faruwa ba.
Hukumar tana jajentawa iyayen wannan jariri bisa ga abin da ya faru.
A Kuma halin da ake ciki an mika wa kwamitin da yake bibiyar matsalolin badakala da sakacin aiki wato (Committee on Negligence of Duty)domin yin zurzurfan bincike tare da daukan mataki akan duk Wanda yake da hannu a cikin wannan sakaci da ya faru.
Shugaban Asibitin Koyarwan farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ya yi kira ga duk Maras lafiya ko Yan Uwan marasa lafiyan da su ga ba su gamsu da yadda ake kula da lafiyar su ko ta Yan Uwansu ba ,da su gaggawa wajen sanar da hukumar Asibitin ta Hanyar jami'anta wadanda ake kira da( Servicom Desk Officers).
Ya ce Asibitin yana da irin wadannan jami'i kimanin Arbanin , wadanda aka raba su a sassan gudanar da aiki daban daban a cikin Asibitin.
Baya ga sashen hurda da Jama'a da wajen Matron Matron na dakin kwanciya wadanda suke aiki tsawon awa ashirin da biyar.
Farfesa Abdurrahman,ya kara da cewa ta Hanyar mika korafi ne kawai hukumar Asibiti za ta iya kamowa tare da hukumta masu laifi.
Ya Kuma Yi kira ga Mahaifin wannan jariri da ya taimaka wajen isar da makamancin wannan korafi ga kwamitin binciken ko Kuma sashen hurda da Jama'a na Asibitin