Posts

Showing posts with the label Kamfanin NNPC

Yanayin Kasuwa Ne Ya Sa Man Fetur Ya Kara Tashi — NNPC

Image
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya danganta tashin farashin man fetur daga Naira 540 zuwa Naira 617 da yanayin kasuwa. Ya bayyana haka ne ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Talata, bayan wata ganawa da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima. “Farashin ya danganta da yanayin kasuwa. Wannan shi ne ma’anar tabbatar da cewa kasuwa ta daidaita kanta. Farashin zai iya hawa kuma a wani lokacin zai iya sauka. Ba batun samar da mai ba ne. “Idan ka je kasuwa, ka sayi kaya, za ka zo kasuwa ka sayar da shi a kan farashin da kasuwa ta ke. Ba shi da alaka da wadatarsa. Mun samu sama da kwanaki 32 muna shigo da mai. Wannan ba matsala ba ce,” in ji shi. Kyari, ya ce abu ne mai kyau ga ‘yan kasuwa su daidaita farashin. “Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa wannan ita ce hanyar da ta dace don daidaita farashin yanayin kasuwa. Ba ni da cikakken bayanai a wannan lokacin, amma na san cewa wannan ba mai dorewa ba ne. Na san cewa kamfanoni da yaw...