Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Ƙasa
Gwamnatin sojin Nijar ta sha alwashin gurfanar da hamÉ“ararren shugaban Æ™asar Mohamed Bazoum kan zargin babban cin amana da kuma zagon Æ™asa ga sha’anin tsaron Æ™asar. Masu juyin mulkin sun ce sun tattara hujjojin da za su yi amfani da su wajen gurfanar da Bazoum da kuma waÉ—anda suka kira muÆ™arrabansa na cikin gida da na Æ™asashen waje. Ministan Matasa da Wasanni, Kanar-Manjo Amadou Abdraman ya sanar a talabijin a ranar Lahadi cewa za su gurfanar da Bazoum da muÆ™arraban nasa ne a cikin Æ™asar Nijar da kuma gaban hukumomin da suka dace na duniya, kan babban cin amanar Æ™asa da yin zagon Æ™asa ga tsaron Jamhuriyar Nijar. Tun ranar 26 ga watan Yuli da sojojin suka yi wa Bazoum juyin mulki suke tsare da shi da matarsa da É—ansa a cikin gidansa. Shugabannin sojojin na iÆ™irarin cewa ba mamaye gidan nasa suka yi ba, domin kuwa yana ci gaba da mu’amala da sauran duniya, kuma likitansa na zuwa ya duba shi a kai a kai, yadda ya saba yi. Wani mashawarcin Bazoum ya tabbatar cewa a ranar Asabar...