Hajj 2023: Shugaban Hukumar NAHCON Ya Gana Da Malamai
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya gana a yau da manyan Malaman Najeriya a hedikwatar hukumar dake Abuja Taron dai an gudanar da shi ne domin tattauna batutuwan da suka shafi ayyukan Hajji na 2023 da kuma samar da kyakkyawar alaka tsakanin NAHCON da malaman addini. Alhaji Zikrullah wanda ya kasance tare da kwamishinonin ayyuka Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa da Kwamishinan kula harkokin ma'aikata da kudi Alhaji Nura Hassan Yakasai da Kwamishinan PRSILS Sheikh Suleiman Momoh, sun godewa Malamai bisa halartar taron da suka yi tare da bayyana irin gudumawar da suke bayarwa ga aikin Hajji. A cikin jawabin nasa, ya jaddada muhimmancin hadin kai tare da neman jagorancin malamai a kan al'amura daban-daban, tare da jaddada shiriya da fadakarwa da suke baiwa alhazai ta hanyar amfani da dimbin ilimi da gogewar da suke da su a cikin lamurran addini da gudanar da aikin hajji, su ma 'yan uwa sun ba da haske da shawarwarin su. Shu