Zaben Adamawa: An Ba Da Belin Kwamishina Hudu
’Yan sanda sun bayar da belin Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, bayan da ya yi kwana uku a tsare a hannunsu. ’Yan sanda sun cafke shi ne kan wata sanarwa mai cike da rudani da ya yi cewa Sanata Aisha Dahiru Binani ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, alhali ba a kammala karbar sakamakon karashen zaben ba. Tun a lokacin INEC ta soke sanarwar, sannan ta bukaci ya gabatar da kansa a hedikwatarta da ke Abuja, amma maimakon ya je, sai ya yi layar zana. Daga bisani hukumar ta rubuta Shugaban ’Yan Sandan Najeriya wasikar neman ya binciki kwamishinan zaben, kan yamutsa hazon da ya yi. Amma wata wasika da ya aike wa shugaban ’yan sanda, Hudu ya ce ya yi sanarwar ne a bisa doka, saboda dalilan tsaro. A ranar Talala ’yan sanda suka sanar cewa sun kama Hudu, wanda ya ce ba ya nadamar sanarwar da ya ya yi cewa Binani ta ci zabe. Amma kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Juma’a cewa rundunar ta bayar da belin kwamishina...