Posts

Showing posts with the label Takunkumi

APC Ta Kano Ta yi Tir Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ganduje, Ta Kuma Sanyawa Shugabannin Mazabar Takunkumi

Image
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ya kakabawa jiga-jigan mazabar Ganduje takunkumi bisa dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce an dakatar da shugabannin unguwar Ganduje na tsawon watanni shidda saboda wasu ayyukan da suka saba wa jam’iyya. Abbas ya ce kwamitin ayyuka na jihar ya yi Allah-wadai da matakin dakatarwar sakamakon amincewa da matakin kwamitin karamar hukumar Dawakin Tofa na jam’iyyar. “Muna da shaidar ganawar da jami’an gwamnatin jihar suka yi da wadanda suka dakatar da shugaban kasa na kasa, kuma kwamitin gudanarwa na jihar ya amince da sanya musu takunkumi na tsawon watanni shida, kuma an dakatar da su,” inji shi. A ranar Litinin din da ta gabata ne shugabannin unguwar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa suka sanar da dakatar da Dakta Ganduje bisa zargin c

Shugaba Bola Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Bude Iyakokin Najeriya Da Nijar Ta Kasa Da Sama Tare Da Dage Sauran Takunkumi

Image
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar tare da dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan take. A sanarwar da mai taimakawa Shugaban kasar kan harkokin yada labarai,  Chief Ajuri Ngelale, yace w annan umarnin ya yi daidai da shawarar da kungiyar ta ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman da ta yi a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja. Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea. Shugaban ya bayar da umarnin a dage takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar nan take: (1) Rufe iyakokin kasa da ta sama tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na ECOWAS a duk jiragen kasuwanci da ke zuwa ko kuma daga Jamhuriyar Nijar. (2) Dakatar da duk wani hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Najeriya da Nijar, da kuma dakatar da duk wasu hada-hadar hidima da suka hada da ayyukan a

PDP Ta Bukaci Sanyawa Buhari Takunkumi

Image
Babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta PDP ta bukaci kasashen duniya da su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari bizar tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga watan gobe, saboda abinda ta kira kalamansa dangane da zaben shugaban kasar da akayi ranar 25 ga watan Fabarairu.  Yayin tsokaci akan zaben, Buhari ya bayyana ‘yan adawar Najeriya a matsayin wadanda suka shantake akan cewar zasu samu nasara ba tare da neman goyan bayan jama’a kamar yadda jam’iyarsa ta APC tayi ba.  Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Debo Ologunagba yace kalaman shugaban na iya tinzira jama’a da kuma haifar da illa ga zaman lafiyar kasar.  Ologunagba ya kuma ce kalaman na iya karfafawa alkalai gwuiwa wajen yanke hukunci akan karar da suka shigar a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben wanda yace tuni wasu a ciki da wajen kasar ke bayyana shi a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya.  Jam’iyyar PDP tace zaben da akayi bana ya gamu da matsalolin da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasa da