Posts

Showing posts with the label Yanke hukuncin Kotu

Darussa Daga Siyasar Kano Ta 2023 - Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

Image
Tun lokacin da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan Kano daga zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar (ta 2023) har izuwa ranar Laraba, 20/9/23, siyasar Kano (wacce ake yiwa taken “sai Kano!”) ta dada zafafa fiye da ko da yaushe a wannan zubin dimokaradiyyar (ta Jamhuriya ta hudu). A bisa fahimtata, dalilai kamar shida ne suka janyo haka.  Za mu yi bitarsu a takaice domin amfanin gaba. 1. Zafin hamaiyar siyasa tsakanin Senator Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ta sa wadannan jagororin na Kano guda biyu sun fifita bukatun kansu, na neman wani ya ga bayan wani a siyasance, fiye da bukatar da Kano take da ita na su hada kansu domin su samarwa da Kano zaman lafiya da cigaba mai dorewa.  A dalilin haka magoya bayansu sun dukufa wajen ganin jagoransu ne a sama ta kowane hali. Don haka cece-kuce ya kazanta a tsakanin juna. Da Allah zai sa idan aka kai karshen tirka-tirkar wadannan manyan biyu su yafewa juna su yi sulhu a tsakani...