Almajiran Abduljabbar Kabara sun ce zasu daukaka kara
Almajiran Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin rataya kan laifin batanci ga Manzon Allah (SAW) suna shirin daukaka kara. Almajiran fitaccen malamin mazaunin Kano, karkashin inuwar A’shabul Kahfi Warraqeem, Reshen Jihar Bauchi, sun yi zargin siyasa a hukuncin da aka yanke masa, saboda a cewarsu, malamnin nasu ya caccaki Gwamnan Jihar Kano, kan zargin almundahana. “Ba mu gamsu da hukuncin ba saboda muna zargin akwai hannun Gwamnan Jihar Kano da wasu malamai da suka dade suna zaman doya da manja da shi (Abduljabbar), wadanda suka yi masa kagen yin batanci domin su kawar da shi daga doron kasa ta hanyar amfani da karfin kotu,” in ji mai magana da yawunsu, Abdullahi Musa a Bauchi. Ya shaida wa manema labarai cewa, “Zargin batancin ba komai ba ne illa neman goga masa kashin kaji daga magauta, ciki har da Ganduje da wasu malamai da ke ganin daukakar da Abduljabbar ke samu a matsayin baraza a gare su.“Shi ya sa suka jefe shi da yin batanci domin su ja masa