Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sanar Da Kudin Aikin Hajjin Bana
A bisa umarnin Hukumar Alhazai ta Najeriya dangane da cikakken shirin aikin Hajjin bana, Darakta-Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alh Laminu Rabi’u Danbappa, a hukumance ya ayyana kudin Hajji na bana Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, inda Darakta janar din ya ayyana Naira miliyan 4.699 a matsayin kudin kujerar aikin Hajin na wannan Shekarar. Wannan sanarwar ta biyo bayan shawarar da hukumar alhazai ta kasa ta yanke a wannan makon. Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya jaddada samun kujerun aikin Hajji domin saye, yana mai kira ga maniyyata da su yi amfani da wannan damar. Ya nanata cewa za’a cika kudin aikin Hajji na karshe daga ranar 3 ga Fabrairu, 2024, zuwa 12 ga Fabrairu, 2024, tare da karfafa wa al’ummar Musulmin da suka yarda kuma suka yi rajista don faranta wa kansu amfani da wannan damar. Bugu da kari, Danbappa yayi kira ga wadanda suka yi ajiya N4. 5m da za su fito da ga...