Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ya Yi Alkawarin Taimakawa Wajen Bunkasa Ilimi
Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya tabbatar wa shugabannin Jami’ar Bayero Kano (BUK) goyon bayan da suke ci gaba da ba su wajen magance kalubalen da ke addabar cibiyar da bangaren ilimi a jihar da ma kasa baki daya. A sanarwar da mashawarcinsa na musammam harkokin yada yada labarani,b Ismail Mudashir ya sanyawa hannu, yace Sanata Barau ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da shugabannin jami’ar karkashin jagorancin mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, suka kai masa ziyarar ban girma a majalisar dokokin kasa, Abuja, a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba, 2023. Mataimakin shugaban majalisar ya yabawa mataimakin shugaban majalisar dattijai bisa goyon bayan da ya bayar tare da neman taimakonsa wajen magance kalubalen da cibiyar ke fuskanta. Musamman, ya yi kira ga Sanata Barau da ya taimaka wajen samar da masauki ga daliban likitanci a yankunan karkara kamar yadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) ta t...