Posts

Showing posts with the label Butu Butu

Labari da dumiduminsa : Jibrin Falgore ya zama kakakin majalisar dokokin Kano

Image
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Rogo a majalisar dokokin jihar Kano, Jibril Samaila Falgore, ya zama shugaban majalisar dokokin jihar. Muhd Bello, mataimakin kakakin majalisar Prime Time News ta tattaro cewa an zabi Falgore a matsayin kakakin majalisar bayan wata tattaunawa da ‘yan majalisar suka yi. Lawal Hussaini,. shugaban masu rinjaye Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin din da ta gabata don kammala tabbatar da sabbin shugabannin majalisar dokokin jihar ya samu halartar gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdusalam Gwarzo, shugaban jam'iyyar na kasa, Engr Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran su. Sabon shugaban majalisar ya fito ne daga mazabar Kano ta Kudu kuma shi ne dan takarar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga shiyyar. Muhd Bello, mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Bello Butu Butu daga mazabar Rimin Gado ya zama mataimakin kakakin majalisar, yayin da mukamin shugaban masu rinjaye ya koma Lawan Husaini na m