Posts

Showing posts with the label Naja’atu Muhammad

Bayan Ficewa Daga Tafiyar Tinubu, Naja’atu Ta Koma Wajen Atiku

Image
  Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano kuma daya daga cikin tsofaffin Daraktocin kamfen din dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad, ta koma wajen dan takarar PDP, Atiku Abubakar. Matakin nata na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan ta sanar da ajiye mukamin na Tinubu, tare da ayyana ficewarta daga jam’iyyar mai mulki. Ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar da ta kai wa Atiku a gidansa ranar Lahadi. Daga bisani dai ta shaida wa  Aminiya  cewa yanzu tana goyon bayan takarar ta Atiku a zabe mai zuwa. A baya dai, Naja’atu, wacce ita ce Daraktar Kungiyoyin Fararen Hula a Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, ta ce za ta gana da ’yan takarar jam’iyyun siyasa kafin ta dauki matsaya kan wanda za ta mara wa baya. Ta ce ta dawo daga rakiyar Tinubu ne saboda a cewarta, sam ba ya iya yin tunani da kansa. Ta ce, “Gaskiya ne yanzu ba na yin Tinubu, dalili ke nan ma da na bar jam’iyyar. Abubuwa da dama sun faru, da kyar yake iya tunani da kwakwalwarsa. Wannan ko shakka babu,