Zan mayar da Wa'adin Sakamakon JAMB Shekara 4 - Sanata Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin tsawaita wa’adin sakamakon jarabawar shiga jami’a (JAMB) zuwa shekaru hudu idan ya ci zaben shugaban kasa.
Majiyarmu ta rawaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Bauchi, lokacin da yake mika tutoci ga ’yan takarar gwamna shida da na Majalisar Dattijai 18 na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ranar Alhamis.
An yi garkuwa da DPO a Filato
Yadda aka yi wa Sakkwatawa kisan gilla a Anambra
Kwankwaso ya ce dalibai da dama na samun sakamako mai kyau a rubuta jarabawar karo na farko, amma da zarar sun rasa gurbi a jami’a sai sun sake sabon lale bayan ba laifinsu ba ne.
“Babu gaira babu dalili an sanya daliban da iyayensu lalubo kudin zana jarrabawa na shekaru biyu koma fiye. Haka ne ya sanya muku ga dacewar sauya haka.
“Haka kuma za mu kirkiri sabuwar dokar dakatar da jarabawar JAMB din na tsawon shekaru hudu, domin ’ya’yanmu su yi amfani da sakamakon wajen samun gurbin karatu a manyan makarantun a wannan tsakanin,” inji shi.
Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi alkawarin maida bada fom din neman gurbi a jami’o’i, da na neman aiki kyauta matukar aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.