Posts

Showing posts with the label Abinci

Gwamna Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa da shirin ciyarwa na watan Ramadan

Image
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin dadinsa kan shirin ciyarwa na watan Ramadan da ake yi a cikin babban birnin Kano. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a. Gwamnan ya ce ya ji takaicin shirin a lokacin da ya kai ziyarar bazata daya daga cikin cibiyoyin ciyar da abinci da ke Gidan Maza, karamar hukumar Municipal. Gwamna Yusuf ya kuma nuna rashin jin dadinsa da yadda masu gudanar da shirin ke gudanar da ayyukansu, wadanda ya ke ganin suna hana wadanda suka ci gajiyar shirin. “Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba, ya zama wajibi a lura da cewa kudaden da aka ware don wannan shiri an tsara su sosai a kowace cibiya” Gwamnan ya yi gargadin. Gwamnan ya gudanar da ziyarar ne biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna nakasu wajen gudanar da shirin ciyarwa a cibiyoyi daban-daban na babban birnin.

Hajj 2014 : Hukumar NAHCON Ta Kafa Kwamitin Bitar Ka'idojin Samar Da Abinci Da Gidaje.

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazari kan wasu sharuddan da suka shafi masauki da abinci don samar da ingantacciyar hidima a lokacin aikin Hajjin 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na Hukumar Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi a wurin taron, mai rikon Shugabancin Hukumar,  Malam Jalal Ahmad Arabi OON, fwc, ya bayyana cewa sake duba ka’idojin da ake da su za su taimaka wajen inganta ayyukan masu ba da hidima wanda hakan zai amfanar da Alhazan Najeriya. A cewarsa, kundin tsarin gudanarwar kwamitin ba sabon sabon abu ba ne, amma wata hanya ce kawai ta yin la'akari da tsarin da ake da shi don samar da kyakkyawan sakamako. “Abin da muke yi yanzu ba wai sabon abu  ba ne kawai don inganta yadda muke yin abubuwa. Kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na duniya, muna bukatar mu kasance da Æ™wazo. Kamar yadda al'ada ce ta duniya, dole ne mu inganta ta hanyoyinmu, don dacewa da mafi kyaw...