Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar tare da dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan take.
A sanarwar da mai taimakawa Shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Chief Ajuri Ngelale, yace wannan umarnin ya yi daidai da shawarar da kungiyar ta ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman da ta yi a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja.
Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.
Shugaban ya bayar da umarnin a dage takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar nan take:
(1) Rufe iyakokin kasa da ta sama tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na ECOWAS a duk jiragen kasuwanci da ke zuwa ko kuma daga Jamhuriyar Nijar.
(2) Dakatar da duk wani hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Najeriya da Nijar, da kuma dakatar da duk wasu hada-hadar hidima da suka hada da ayyukan amfani da wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar.
(3) Daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar a Babban Bankin ECOWAS da kuma daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar, da kamfanonin gwamnati, da ma'aikatu a bankunan kasuwanci.
(4) Dakatar da Nijar daga duk wani tallafi na kudi da mu'amala da duk hukumomin kudi, musamman EBID da BOAD.
(5) Hana tafiye-tafiye ga jami'an gwamnati da 'yan uwansu.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da dage takunkumin kudi da tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Guinea.