Posts

Showing posts with the label Zamfara

Na shiga matsananciyar damuwa da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan - Gwamnan Zamfara

Image
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Inda yace "A madadin gwamnatin Jihar Zamfara, ina miÆ™a saÆ™on ta'aziyya da jaje ga al'ummar Æ™aramar hukumar Zurmi, musamman iyalai da ‘yan uwan waÉ—anda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da 'yan bindiga suka kai garin"  Ina son tabbatarwa da al'umma cewa gwamnatina za ta bayar da tallafi da agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa. Sannan ina mai tabbatar da cewa muna nan jajirce akan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar Zamfara baki É—aya. Ina sane da sadaukarwar da jami’an tsaro suke yi a Æ™oÆ™arin da suke na kare rayukan al’umma, gwamnatina za ta ba su duk wasu kayan aiki da kuma tallafin da suka dace domin yaÆ™ar ‘yan bindiga, ba za mu huta ba har sai Zamfara ta samu cikakken tsaro insha Allahu.   WaÉ—annan sabbin hare hare sun biyo bayan nasarar da jami'an tsaro suka samu ne, na kashe shugabannin 'yan ta'addan. Ciki har da nasarar ...

’Yan Bindiga Sun Sako 70 Daga Cikin Yara 85 Da Suka Sace A Zamfara

Image
  ’Yan ta’adda da suka yi garkuwa da yara sama da 85 a Jihar Zamfara sun sako 70 daga cikin yaran, amma sun kashe biyu. A ranar Juma’a ’yan ta’addan suka sako yaran, kimanin mako uku bayan sun sace su daga kauyen Wanzamai na Karamar Hukumar Tsafe ta jihar. Wani mazaunin yankin Sani Aliyu ya ce, “Yara biyu da ’yan bindigar suka kashe sun yi kokarin tserewa ne, wadanda aka sako din kuma sun galabaita saboda tsananin yunwa, kuma yanzu ana duba lafiyarsu.” Ya ce ganin irin galabaitan da yaran suka yi ya sa iyayensu koke-koke, kuma “An sako su ne bayan an biya kudin fansa Naira miliyan shida; da farko miliyan uku aka ba su, amma suka ki sako su, sai an kara musu da sabbin babura guda biyu.” Sai dai ya bayyana cewa duk da haka, akwai karin wasu yaran a hannun ’yan ta’addan, “ba mu san dalilin da suka ki sako su ba.” Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bangaren Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, amma hakarsa ta yin magana da kakakin rundunar, CSP Muhammad Shehu, ba ta cim ma ruwa ba. Kimanin ...

Tinubu Ya Yi Alawadai Da Harin 'Yan Bindiga A Zamfara, Kano Da Katsina is a Tare Da Jajantawa Wadanda Abun Ya Shafa

Image
Tinubu ya kuma yi ta'azziya ga iyalan Abacha da na Sheikh Gumi  Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da kuma garin Maigari na karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano a karshen mako. Rahotanni sun ce an kashe jami’in ‘yan sanda na Dibision (DPO), sufeto ‘yan sanda da dan banga a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara. A harin na Kano wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun shiga gidan wani basarake inda suka harbe shi har lahira. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar a ranar Litinin, Tinubu ya ce harin da aka kai a garin Maru bayan an samu zaman lafiya a jihar Zamfara, abin tunatarwa ne cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya. “A matsayinmu na kasa dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan ‘yan kasuwa na mutuwa da ta’addanci gaba daya, kashe-kashe...

Matawalle ya dakatar da yakin neman zaben APC a Zamfara

Image
Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya dakatar da yakin neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara har zuwa ranar 18 ga watan Janairu da muke ciki. Rohotanni sun bayyana cewa kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar ya dakatar da harkkokin kamfe din gwamnan ne don mayar sa hankali kan zaman lafiya a jihar. “Na yi alkawarin mayar da hankali wajen dawo da zaman lafiya a mulkina na biyu a Jihar Zamfara,” cewar Matawalle. Aminiya ta ruwaito cewa Ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar ta kaddamar da yakin neman zabensa a Karamar Hukumar Kaura Namoda, a ranar 27 ga watan Disamba, 2022. Matawalle dai ya nada tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabensa. A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar ya ce matsalar tsaro za ta inganta idan Matawalle ya sake darewa kujerar mulkin jihar a karo na biyu. Yari, wanda ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben APC zuwa kamfe din jam’iyyar ya ce zai goyi bayan takarar Matawalle dari bisa dari.

’Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Kanar Din Soja A Zamfara

Image
  ’Yan bindiga sun sace Kanar Lawal Rabiu Yandoto (mai ritaya) a kan hanyarsa ta zuwa garinsu, Yandoto da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Wata majiya ta bayyana cewa ’yan bindigar sun sace shi ne tare da ’ya’yansa biyu da kuma wasu. “Maharan sun yi wa Kanar kwanton bauna da misalin karfe 6 na yamamcin ranar Lahadi, suka sace shi tare da ’ya’yansa biyu da kuma wasu mutum biyu,”  in ji majiyar. Majiyar ta ce an ji karar harbe-harbe daura da shiga garin na Yandoto lamarin da ya tilasta mutane guje-guje domin tsira. Ta bayyana cewa an gano maharan sun yi awon gaba da tsohon Kanar din ne bayan da mutane suka samu motarsa babu kowa a ciki. Kakakin ’yan sandan jihar bai daga waya ba ballatana a ji ta bakinsa kan lamarin. (AMINIYA)