Posts

Showing posts with the label Sallah

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Ranakun Hutu

Image
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah. Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar, Aishetu Ndayako ya fitar ranar Lahadi. Ministan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma. Tunji-Ojo ya yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan dabi’u da suka hada da kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, makwabtaka, tausayi, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da misali da shi. (SOLACEBASE)

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Talatin Lokacin Sallah A Zamfara

Image
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na Asuba, a lokacin da ake shirin fara salla. Garba ya ce, “Za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ’yan bindiga suka shigo masallaci suka umarci kowa ya fito ya bi su. “Kowa ya yi kokarin guduwa domin tsira amma suka tare ko’ina suka gargade mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa. “Na samu na iya tsalle daga tagar kuma da sauri na shiga wani kango da ke kusa da masallacin na boye kaina,” in ji shi. Shaidan ya bayyana cewa ’yan bindigar sun bar baburansu a nesa da masallacin don kada a lura da motsinsu. Ya kara da cewa, “Daga baya sun tafi da mutanen zuwa inda baburansu suke, suka tafi da su.” A cewarsa, adadin mutanen da aka sace a masallacin zai iya wuce 30. Ya kara da cewa “masallacin ya cika a lokacin da suka kai hari kuma kadan ne daga cikin mu suka samu tsira.” Daya daga cikin shugabannin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin ’yan bindiga...

Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Gudanar Da Taron Shan Ruwa Na Mutum Dubu Biyu

Image
Zababben Dan majalisar  tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji) ya jagoranci taron shan ruwa da al'umar Kiru da Bebeji mutane 2000 a gidansa dake garin Kofa. Bayan buda baki Kofa ya jagoranci mahalatta wannan taro Sallah.  Taron shan ruwan ya sami halartar Dagatai, Limamai, 'Yan siyasa, da sauran mutane daban-daban dake mazabarsa ta dan majalisar tarayya  Yayin taron, anyi amfani da wannan dama wajen yi wa Zababben Dan Majalisar Tarayyar, Alhaji Abdulmumin Jibrin Kofa addu'a da  Gwamna jihar Kano mai jiran rantsuwa Injiniya Abba Kabir . Yusif tare da Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Haka kuma an roki madaukakin Sarki Allah ya dauwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jahar Kano da ma Najeriya baki daya

Gwamnati ta karrama limamin da ya tausasa kyanwa a Salla

Image
  Gwamnatin Algeria ta karrama limamin nan, Imam Walid Mehsas wanda kyanwa ta dare jinkinsa a daidai lokacin da yake jagorantar Sallar Taraweeh, inda cikin tausasawa ya yi ta shafar kwanyar wadda ta sunbace shi kafin daga bisani ta sauka daga jikinsa don ratsin kanta. Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ne ya nuna yadda Imam Walid ya mu’amalanci kwanyar cikin kyawun yanayi, lamarin da ya kayatar da jama’a da dama hatta wadanda ba Musulmai ba daga sassan duniya. Limamin ya sha yabo da jinjina, yayin da manyan kafafen yada labarai na duniya suka yi ta yada wannan labarin. Yanzu haka gwamnatin Algeria ta gayyace shi tare da shirya masa taron liyafa na musamman, inda Ministan Kula da Lamurran Addini na Kasar, Dr. Youssaf Belmahdi ya yaba masa kan wannan kyakkyawar dabi’ar da ya nuna wa dabba. RFI