INEC ta ce zata gurfanar da iyayen yaran da aka kama suna kada kuri'a

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. Hukumar zaben Najeriya ta ce matukar aka samu kananan yara da ke kokarin kada kuri’a a lokacin zabuka masu zuwa, to lalle kuwa za a kama tare da gurfanar da iyayensu a gaban shari’a. Wannan dai na kunshi ne a wani sakon gargadi da hukumar zaben ta fitar, a ci gaba da daukar matakai domin hana magudi a zabukan da za a yi cikin wanna shekara. Domin sauraron cikakken rahoto kan wannan batu tare da Muhammad Kabiru Yusuf, shiga alamar sauti