Kwamitin Karbar Mulki Na NNPP Na Kano Ya Zargi Gwamna Ganduje da gurgunta Tsarin Karbar mulki
Kwamitin Karbar Mulki na jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado da yin zagon kasa ga tsarin mika mulki ga gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf mai jiran gado. A cewar shugaban kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP, Farfesa Abdullahi Baffa Bichi, gwamnatin Ganduje ta nuna turjiya da rashin hadin kai tun bayan kafa kwamitin mika mulki na NNPP da zababben gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi. Jaridar Nigerian Tracker ta rawaito Bichi yana bayyana cewa kwamitin mika mulki na NNPP ya kafa kananan kwamitoci 33, amma babu daya daga cikin kwamitocin da ya samu hadin kai daga gwamnatin Ganduje. Duk da yunkurin kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP na shirya taron hadin gwiwa da kwamitin mika mulki na gwamnati mai barin gado, gwamnatin Ganduje ta bukaci su zabi mutane uku ne kawai a taron wanda jam’iyyar NNPP ba ta amince da shi ba. Bichi ya zargi Gwamna Ganduje da mayar da dukkan sakatarorin dindindin na jihar a wani bangare na koka...