An Sako Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ekiti

An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su Dalibai tara da malamansu da aka yi garkuwa da su a Jihar Ekiti sun kubuta daga hannun ’yan bindiga. Da misalin karfe 2 na dare, kafin wayewar garin yau Lahadi ne masu garkuwa da su suka sako su. Hukumomi a jihar sun tabbatar da sako daliban su tara tare da malamansu. An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti. Kawo yanzu dai babu bayanin ko an biya kudin fansa. An yi garkuwa da su ne a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti. (AMINIYA)