Posts

Showing posts with the label Ingila

Malaman Makaranta Sun Fara Yajin Aiki A Ingila Kan Karin Albashi

Image
Malaman makaranta a Ingila da yankin Wales sun sanar da tsunduma yajin aiki daga watan Fabrairu mai zuwa saboda karin albashi. Kungiyar malaman mai suna (NEU) ta ce mambobinta sun amince da gagarumin rinjaye a fara yajin aikin har sai an yi musu karin da zai yi daidai da yanayin hauhawar farashin kayayyaki a kasar. Bayan wata 11, farashin kayayyaki ya sauka a karshen 2022 a Najeriya – NBS Kotu ta yanke wa mutum 6 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ma’aikatan gwamnatin kasar da dama ke guna-guni kan karancin albashi. “Mun tabbatar gwamnati ta san akwai bukatar a gyara albashin malaman makaranta,” in ji Kevin Courtney, Babban Sakataren NEU, yayin wani taron kungiyar da aka watsa kai tsaye. Shugabannin kungiyar dai na shirin ganawa da Ministan Ilimin kasar ranar Laraba. Shi ma wani Sakataren kungiyar, Mary Bousted, ya ce, “Sun san ba da wasa muke ba. Da gaske muke yi wajen kokarin kare ayyukanmu.” Kungiyar dai ta sanar da f

Za a haramta amfani da cokali da farantin soso a Ingila

Image
Gwamnmati a Ingila ta tabbatar da cewa za ta haramta kayan cin abinci waɗanda ake amfani da su sau ɗaya ana jefarwa, kamar cokali da farantan soso. Ba a san yaushe ne harmacin zai fara aiki ba, amma hakan na zuwa ne bayan irin wannan yunƙuri a yankunan Wales da Scotland. Sakatariya mai kula da harkar muhalli, Therese Coffey ta ce za a yi hakan ne saboda a kare muhalli domin amfanin al'ummar da za ta zo nan gaba. Masu hanƙoro sun yi maraba da shirin, sai dai sun buƙaci a ɓullo da ƙarin hanyoyin rage amfani da robobi Alƙaluma sun nuna cewa a ƙasar ta Ingila kowane mutum na amfani da aƙalla farantin cin abinci na roba guda 18 da kuma cokula da wuƙaƙen cin abinci 37 a kowace shekara, inda kashi 10% na irin waɗannan robobi ne kawai ake sake sarrafa su.