Posts

Showing posts with the label Hajiya

Hajiyar Kano guda daya ta rasu bayan aiwatar da aikin hajji

Image
Hadiza Ismail daga karamar hukumar Madobi ta rasu a ranar Litinin kusan da 3:15 PM Saudi na gida bayan gajeriyar rashin lafiya. A sanarwar da jagoran tawagar 'yan jaridun Kano na aikin hajjin bana, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce an kai Hajiyar ce zuwa Asibitin NAHCON don magance zazzabi kafin a tura ta zuwa Asibitin Sarki Abdiziziz, Makkah a inda aka tabbatar da rasuwarta. Tuni aka binne ta a Makkka bayan sallar jana'izar a cikin Masallacin Ka'aba. Darakta Janar na hukumar alhazai na jihar kano, Alhaji Lamanu Rabiu Rabiu DanbAPPA ya tabbatar da labarin rasuwar.  A madadin gwamnatin Kano, Danbaffa yayi adduar Allah ya Ji kanta ya kuma bawa iyalanta hakurin jure rashin da suka yi