Posts

Showing posts with the label Kungiyar Fararen Hula

Hajj 2024: Kungiyar Fararen Hula Ta Yi Kira Ga Babban Bankin Najeriya Ya Sauya Tunani Kan Biyan Kudin Guzurin Alhazai

Image
An shawarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya yi watsi da ra’ayin bayar da kudin  (BTA) ta hanyar katin biyan kudi. Kungiyar fararen hula masu daukar rahotannin aikin Hajji  (IHR) ne suka bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da babban jami'inta na kasa Ibrahim Mohammed ya fitar. Kungiyar ta ce kasa da sa’o’i 24 da fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, babban Bankin ya umarci wasu bankunan kasuwanci da su biya maniyyatan dala 200 kacal daga cikin dala 500 da ake sa ran kowane mahajjaci zai samu yayin da sauran dala 300. za a bayar a kan katin cirar kudi  “Alhazai na bana sun riga sun shiga cikin rashin tabbas da yawa tun daga manufofin sayayya da suka haifar da hauhawar farashin Hajji zuwa raguwar kudin guzuri. Wannan shawarar da babban bankin ya yanke zai kara musu bala’i ne kawai”. “ Sanin kowa ne cewa mafi yawan alhazanmu sun fito ne daga karkara kuma ba su da masaniyar harkar hada-hadar kudi, yawancin ma ba su san yadda ake amfani da katin ATM...