Posts

Showing posts with the label satar mutane

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Talatin Lokacin Sallah A Zamfara

Image
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na Asuba, a lokacin da ake shirin fara salla. Garba ya ce, “Za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ’yan bindiga suka shigo masallaci suka umarci kowa ya fito ya bi su. “Kowa ya yi kokarin guduwa domin tsira amma suka tare ko’ina suka gargade mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa. “Na samu na iya tsalle daga tagar kuma da sauri na shiga wani kango da ke kusa da masallacin na boye kaina,” in ji shi. Shaidan ya bayyana cewa ’yan bindigar sun bar baburansu a nesa da masallacin don kada a lura da motsinsu. Ya kara da cewa, “Daga baya sun tafi da mutanen zuwa inda baburansu suke, suka tafi da su.” A cewarsa, adadin mutanen da aka sace a masallacin zai iya wuce 30. Ya kara da cewa “masallacin ya cika a lokacin da suka kai hari kuma kadan ne daga cikin mu suka samu tsira.” Daya daga cikin shugabannin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin ’yan bindiga

Canjin Kudi Ya Rage Satar Mutane Da Karbar Rashawa —Malami

Image
Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa canjin kudi ta Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi ya taimaka wajen rage aikata ayyukan garkuwa da mutane. Malami, ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon Tarayya da ke Kaduna, inda ya ce jama’a ba sa ganin nasara da tsarin ya haifar. Da yake bayyana hakan a ranar Juma’a, Malami ya ce: “Na fada muku maganar tana gaban kotu, ba za mu bijire wa kotu ba, za mu bi umarnin kotu amma muna da ’yancin fada wa kotu alfanun da tsarin ya haifar. “Idan ba ku ga amfanin tsarin ba, ya kamata kuma a gefe daya ku ga alfanunsa. “Idan wadancan gwamnonin sun bayyana wa kotu wahalar da ake sha saboda tsarin, ya kamata kuma a fahimci cewa tsarin a gefe daya yana warware wasu matsalolin. “Na ba ku misali da matsalar tsaro; Tun bayan da aka kaddamar da wannan tsarin garkuwa da mutane ya ragu. “Sannan ya rage yawan cin hanci da rashawa, don haka muna da ’yancin zuwa mu bayyana wa kotu amfanin