Posts

Showing posts with the label Fagen Siyasa

Idan Mijina ya Gza bayan Shekara hudu, Ka da ku Sake Zabarsa - Matar Tinubu

Image
  Mai dakin dan takarar Shugaban Kasa na jam ’ iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci  ’ yan Najeriya da kada su sake zaben mijinta a karo na biyu idan ya gaza tabuka komai bayan shekara hudu. Oluremi ta yi wannan kira ne a wajen gangamin yakin neman zaben Tinubu/Shettima na matan shiyyar Kudu maso Gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin Jihar Imo. Ta ce, “A ajiye batun addini a gefe, ni Kirista ce. Ko kun taba tunanin cewa wata rana za a samu ‘yan takara Kirista da Kirista? “Me ya kamata ya zama madogara? Tun da mun jarraba ‘yan takara Musulmi da Kirista, bari mu jarraba wannan ma mu gani sannan bayan shekara hudu idan ba su tabuka komai ba kuna iya yin waje da su,” in ji ta. Ta kara da cewa, bai kamata addinin mutum ya zama abin damuwa a sha’anin zabe a Najeriya ba, maimakon haka kamata ya yi a yi la’akari da tsoron Allah da dan takara ke da shi. Saboda a cewarta, “Idan ana da mutum mai tsoron Allah, ba wai Kirista ko Musulmi ba, amma dai mutum mai tsoron Allah....