Posts

Showing posts with the label Hutu

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Ranakun Hutu

Image
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah. Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar, Aishetu Ndayako ya fitar ranar Lahadi. Ministan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma. Tunji-Ojo ya yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan dabi’u da suka hada da kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, makwabtaka, tausayi, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da misali da shi. (SOLACEBASE)

Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Hutun Bikin Takutaha

Image
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ayyana yau Laraba 4 ga Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. A Cikin sanarwar da Kwamishinan yada labarai na Kano, Injiniya Abba Malam Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu, Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokutan bukukuwa domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum. Ya kuma bukaci jama’a da su rika yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a Kano a Najeriya baki daya. Ya yi addu’ar Allah ya ganar damu wannan lokaci mai wuya, ya kuma sa mu dace a wannan damina da kuma damina mai zuwa.