Posts

Showing posts with the label Hukumar kididdiga ta kasa

Rashin Aikin Yi Ya Ragu Da Kaso 4.1 A Najeriya – Hukumar Kididdiga

Image
Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce matsalar rashin aikin yi ta ragu da kaso 4.1 cikin 100 a watanni uku na farkon 2023. Alkaluman rashin aikin yi dai sun kai kaso 33.3 cikin 100 a rahoton karshe da hukumar ta fitar ya zuwa karshen shekara ta 2020. A cewar Babban Mai Kididdiga na Kasa, Semiyu Adediran, sun yi amfani da tsarin ICLS ne wajen yin kididdigar ta karshe. Taron masu kididdigar kwadago ta duniya ne ya kirkiro sikelin da aka yi amfani da shi a shekara ta 1982. A baya dai hukumar ta ce za ta yi amfani da sabuwar hanya wajen kididdige ainihin yawan masu aikin yi da masu zaman kashe wando domin samun sahihan alkaluma a Najeriya. A yayin da yake jawabi yayin kaddamar da sabuwar hanyar kididdigar a Abuja ranar Alhamis, Semiyu ya ce sabbin alkaluman sun sa kididdigar ta Najeriya ta zama iri daya da ta sauran ƙasashen duniya. Ya ce an gudanar da ita ne da hadin gwiwar Bankin Duniya da Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO), kuma tuni ƙasashe 26 suka rungume ta a nahiyar Af...