Shugaban Tinubu ya amince da tsarin Biyan Tiriliyan 3.3 Domin Mayar Da Ingantacciyar Wutar Lantarki
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da tsarin biyan kuɗaɗe domin kammala biyan bashin da ake bin bangaren wutar lantarki a ƙarƙashin Shirin Gyaran Harkokin Kuɗi na Fannin Wutar Lantarki na Ƙasa. A sanarwar da mai bawa Shugaban kasa Shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, yace wannan tsarin biyan bashin ya biyo bayan cikakken nazari na ƙarshe kan tsofaffin basussuka da suka addabi bangaren wutar lantarki fiye da shekaru goma. Basussukan sun taru ne tsakanin watan Fabrairu na shekarar 2015 zuwa Maris na shekarar 2025. Bayan tantancewa, an amince da jimillar Naira tiriliyan 3.3 a matsayin cikakken biyan bashin, domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen warware matsalar. An fara aiwatar da shirin, inda tashoshin samar da wutar lantarki guda 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar biyan bashin da ya kai Naira tiriliyan 2.3. Gwamnatin Tarayya ta riga ta samar da Naira biliyan 501 domin fara biyan kuɗaɗen. Daga cikin wannan adadi, an riga an fitar da ...