Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Bauchi, Ta Jaddada Kudirinta Na Yin Hadin Gwiwa Da Masu Ruwa Da Tsaki Don tunkarar
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, ta jaddada kudirinta na yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta a aikin Hajjin shekarar 2024. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar mata musulmi ta Najeriya FOMWAN reshen jihar Bauchi a ziyarar ban girma a ofishinsa. Ya bayyana FOMWAN a matsayin kwararre kuma ya amince da rawar da suke takawa wajen hada hanyoyin sadarwa tsakanin hukumar da alhazai. Imam Abdurrahman ya jaddada cewa hukumar a shirye take ta ba da hadin kai ga duk wata kungiya ko jama'a da ke son bayar da gudummawar kasonta don samun nasarar aikin Hajji. A nata jawabin Amirah FOMWAN reshen jihar Bauchi wanda Haj ta wakilta. Aishatu Shehu Awak wadda ta zama shugabar kungiyar FOMWAN kuma shugabar kwamitin daawa ta jihar Bauchi, ta ce sun je hukumar ne domin