Posts

Showing posts with the label Garkuwa

’Yan Bindiga Sun Sako 70 Daga Cikin Yara 85 Da Suka Sace A Zamfara

Image
  ’Yan ta’adda da suka yi garkuwa da yara sama da 85 a Jihar Zamfara sun sako 70 daga cikin yaran, amma sun kashe biyu. A ranar Juma’a ’yan ta’addan suka sako yaran, kimanin mako uku bayan sun sace su daga kauyen Wanzamai na Karamar Hukumar Tsafe ta jihar. Wani mazaunin yankin Sani Aliyu ya ce, “Yara biyu da ’yan bindigar suka kashe sun yi kokarin tserewa ne, wadanda aka sako din kuma sun galabaita saboda tsananin yunwa, kuma yanzu ana duba lafiyarsu.” Ya ce ganin irin galabaitan da yaran suka yi ya sa iyayensu koke-koke, kuma “An sako su ne bayan an biya kudin fansa Naira miliyan shida; da farko miliyan uku aka ba su, amma suka ki sako su, sai an kara musu da sabbin babura guda biyu.” Sai dai ya bayyana cewa duk da haka, akwai karin wasu yaran a hannun ’yan ta’addan, “ba mu san dalilin da suka ki sako su ba.” Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bangaren Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, amma hakarsa ta yin magana da kakakin rundunar, CSP Muhammad Shehu, ba ta cim ma ruwa ba. Kimanin ...

’Yan Bindiga Sun Sace Manoma 100, Sun Sanya Haraji A Neja

Image
  ’Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum fiye da 100 ciki har dakanan yara a Kananan Hukumomin Rafi da Mashegu na Jihar Neja. Daga cikin wadanda bata-garin suka kashe har da basaraken gargajiya da ’yan banga biyu da wani mutum daya a Karamar Hukumar Mashegu. Maharan sun kuma sanya harajin Naira miliyan uku-uku domin dakatar da garkuwa da mutane a yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro inda suka yi awon gaba da mutum 61. Al’ummar yankunan Rafi da ’yan bindiga suka kai wa hari sun shiga yin kaura zuwa wasu wurare domin samun aminci. Rahotanni sun bayyana cewa a mako uku da suka gabata mahara sun far wa kauyuka 14 a kananan hukumomin, inda suka sace yawancin mutanen a gonakin wake,  marasa da dawa. Wani mazaunin yankin ya ce sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a yi garkuwa da su, a yayin da ’yan bindiga ke sace masu amfanin gona. 'Yan Bindiga Garkuwa noma