Shirin Aikin Hajji Na 2023 Yana Ci Gaba Da Samun Nasara - NAHCON
Aikin Hajjin 2023 daga Najeriya ya shiga kwana na bakwai inda kawo yanzu an samu tashin jirage sama da 33. A jihohin Filato da Benuwai da Nasarawa an kammala jigilar maniyyatan nasu ta jirgin sama yayin da sauran jihohin ma ke samun ci gaba. Idan dai ba a manta ba hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kara yawan jiragenta zuwa biyar a bana. A sanarwar da mataimakiyar Daraktar harkokin hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara, tace Sai dai hukumar ta NAHCON ta amince da cewa wata matsala ta fasaha ta shafi daya daga cikin jiragen da hukumar ta samu kwangilar jigilar alhazan jihar Jigawa zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023. Matsalar da aka samu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya tilasta wa jirgin sauka na wani dan lokaci a filin jirgin saman Aminu Kano da ke Jahar Kano. Yayin da lamarin ya haifar da tsaikon da babu makawa, ko shakka babu shugaban hukumar Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya tabbatar wa alhazan Najeriya musamman wadanda...