Posts

Showing posts with the label Rashin Lafiya

Rashin Lafiyar Buhari Ta Kawo Wa Gwamnatinsa Cikas —Adesina

Image
Mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce rashin lafiyar da Shugaban Kasa ya yi a 2017 ta janyo wa gwamnatinsa nakasun aiki na watanni takwas a mulkinsa. Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zanta wa a gidan talabijin na Channels. Adesina, wanda ya bayyana nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a yayin zantawar, ya ce shugaban ya shafe watanni takwas yana jinya a Ingila a 2017. “Lokacin da ya soma rashin lafiya a watan Janairun 2017, ya dawo a watan Maris, ya sake komawa a watan Afrilu kuma bai dawo ba sai 19 ga watan Agusta. “Wannan jinya ta dauki wata takwas ba tare da yana aiwatar da komai ba. Tabbas, babu wanda zai so hakan amma abun farin ciki shi ne daga baya ya samu lafiya.” Sai dai ya ce duk da wannan koma baya da aka samu, shugaba Buhari zai bar kasar nan cikin nagarta fiye da yadda ya same ta. Adesina ya bayyana cewa a shekarar 2015 lokacin da Buhari ya karbi mulki, kananan hukumomi 1...