Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tantance Lafiya Kafin Aure A Kano
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure. Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka da su ba. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar tana ganin ya zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara masu fama da matsalolin lafiya kamar su sickle cell anemia, HIV/AIDS, da hepatitis. Wannan shiri dai ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga fannin kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadi. Dokar ta wajabta yin gwajin tilas na HIV/AIDS, Hepatitis, genotype, da sauran abubuwan da suka dace kafin aure. Har ila yau, ya haramta duk wani wariya ko kyama ga mutanen ...