Tawagar Farko Ta Jami'an NAHCON Sun Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
Tawagar Farko ta jami'an NAHCON 31 a yau sun tashi zuwa kasar Saudiyya daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja. Tawagar da ta kunshi jami’an hukumar NAHCON 21 da ma’aikatan lafiya 10 za su je kasar Saudiyya domin shirye-shiryen karshe na karbar alhazan Najeriya daga jihar Nassarawa wadanda za su isa Masarautar a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2023. A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Mousa Ubandawaki, tace Tawagar dai za ta tsara tare da daidaita liyafar, masauki, ciyarwa da sufuri, lafiya da jin dadin alhazai a duk tsawon lokacin aikin Hajji karkashin jagorancin mataimakin daraktan horaswa, Alhaji Ibrahim Idris. A wani takaitaccen biki na bankwana da aka gudanar a ofishin hukumar gabanin tashinsu zuwa kasa mai tsarki, Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana aikin Hajji a matsayin wani lamari d