Posts

Showing posts with the label Fasfo

EFCC Ta Kwace Fasfon Sadiya Da Betta Edu

Image
Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar. Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadi ya  ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken. “Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu. “Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar. Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata. Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta. Aminiya  ta ruwaito cewa Edu ta isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata domin amsa...